Isa ga babban shafi
Saudi Arabia

Iran ta bukaci shiga cikin komitin binciken hatsarin jifar Shedan

Kasar Saudia na ci gaba da shan suka kan shirin aikin hajin bana, da ya hadu da cikas a birnin Makah. Tuni dai Kasar Iran da ta yi hasarar yan kasarta 131 a cikin turmitsitsin da ya goce a ranar shekaranjiya alhamis, inda mutane 717 suka rasa rayukansu, ta zargi kasar Saudia da zama ummal-haba’isar faruwar hatsarin.

Les images de cadavres de pèlerins entassés et recouverts d'un simple drap ont beaucoup choqué.
Les images de cadavres de pèlerins entassés et recouverts d'un simple drap ont beaucoup choqué. REUTERS/Stringer
Talla

Kasar Iran dai ta bukaci mahukumtan kasar Saudia su sakata cikin kwamitin da zai binciki gano musabbabin al’amarin da ya haddasa faruwar hatsarin, a wajen jifar shedan na Mina dake kusa da birnin Makah a ranar alhamis da ta gabata.

Shi dai, wannan zargi da Iran ta yi ga Saudia, ana ganin zai iya sake tado tsohuwar gabar dake da akwai tsakanin manyan kasashen musuluncin 2, dake yankin gabas ta tsakkiya

Iran dai, da ke biyar mazahabar shi’a, da kuma Saudia Bawahabiya ‘yar sunni, na ci gaba da takun sakar siyasa, da addini marar dadi a tsakaninsu ne, tun lokacin faruwar juyin juya halin Musuluncin 1979 a kasar ta Iran har zuwa yau.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.