Isa ga babban shafi
Amurka-Iran

Gangamin adawa da yarjejeniyar Nukiliyar Iran a Washington

Daruruwan mutane a birnin Washington na Amurka sun hada gangami domin nuna adawa da yarjejeniyar nukiliya da manyan kasashen duniya suka kulla da Iran.Wasu ‘yan takarar shugaban kasa a bangaren Jam’iyyar adawa ta republican ne ke jagorantar zanga-zangar ta nuna adawa da gwamnatin shugaba Barack Obama kan yarjejeniyar nukiliyan Iran.

AFP PHOTO/BRENDAN SMIALOWSKI
Talla

Senatocin Amurka guda biyu Ted Cruz da Donald Trump da ke takarar shugaban kasa a bangaren Jam’iyyar Republican ke jagorantar zanga-zangar ta nuna adawa da yarjejeniyar Nukiliya da manyan kasashen duniya guda 6 suka amince da Iran.

Dubban mutane ne suka hada gangamin a birnin Washington suna masu kira ga al’ummar yahudawa su yi allawadai da yarjejeniyar.

A cewar su yarjejeniyar barazana ce ga rayuwar Amurkawa da kuma Isra’ila.

Attajirin Amurka Dolad Trump kuma dan takarar shugaban kasa a a jam’iyyar adawa ta republican ya caccaki yarjejeniyar ta Iran.

Trump ya ce idan har ya lashe zaben shugaban kasa zai dawo da martabar Amurka wajen kulla yarjejeniyar da ta dace sabanin ta Iran.

Amurka dai tare da Faransa da Birtaniya da Jamus da Rasha da China ne suka amince su janye wa Iran takunkumin kariyar tattalin arziki idan ta dakatar da shirinta na nukiliya.

Amma bangaren Republican na adawa da yarjejeniyar wadanda suke ganin akwai batutuwa da dama da yarjejeniyar ba ta tabo ba.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.