Isa ga babban shafi
Amurka

Maganin Aspirin na iya rage barazanar cutar kansar tunbi

Sabon bincike na cewa Maganin rage radaddi na asipirin na iya rage barazanar kamuwa da cutar kansar tunbi kamar yadda  wata Mujallar kasar Amurka ta wallafa.

Talla

Teba ko kiba matsala ce da ka iya haifar da cutar kansar tunbi musanman ga wasu mutane acikin al’umma dake dauke da kwayar hallita ta daban, sai dai kuma kamar yadda binciken da aka wallafa a mujallar Journal ke cewa shan maganin aspirin na iya magance wannan matsalar ta kansar Tunbi.

An kuma tabbatar da hakan ne bayan gwaje gwajen da aka yi akan wasu mutane 937 dake da irin wannan launin kwayar hallita a kasashe 16 a tsawon shekaru goma kafin a tabbatar da tasirin maganin aspirin akan cutar.

John Burn daya daga cikin wadanda suka jagoranci bincike ke cewa kiba ko teba dai na daga cikin cututukan da ke haddasa cutar kansar Tunbi kuma shan aspirin a cewar sa na iya rage raddadin cutar .

Yanzu dai masanan na kokarin sake wani sabon gwajin maganin aspirin akan wasu mutane dubu uku daga sassan duniya domin tabbatar da ingancin sa akan cutar kansar tunbin.

Wannan sabon binciken akan tasirin da maganin aspirin ka iya yi ga cutar kansar tunbi ya kara harzuka masana wajen kaddamar da sabin gwaje gwaje domin sanin dalilan dake haifar da cutar kansa baki daya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.