Isa ga babban shafi
Amurka-Cuba

Cuba na bin Amurka bashin miliyoyin daloli

Tsohon Shuagban kasar Cuba Fidel Castro wanda yayi bikin cika shekaru 89 a duniya, ya ce Cuba na bin Amurka bashin miliyoyin daloli saboda takunkumin kasuwancin da ta kakabawa kasar na shekaru 50.

tsohon Shugaban Cuba Fidel Castro rike da wata Jarida
tsohon Shugaban Cuba Fidel Castro rike da wata Jarida REUTERS/Alex Castro/Courtesy of Cubadebate
Talla

Castro ya bayyana haka ne a kasidar da ya wallafa a jaridun kasar, kwana guda kafin Sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry ya ziyarci kasar.

Amurka ta sanyawa Cuba takunkumi ne a shekarar 1962 bayan Castro ya kwace mulki daga hannun gwamnatin da take goyawa baya, abinda ya sa ta kakaba mata takunkumi.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.