Isa ga babban shafi
Amurka-Cuba

Amurka da Cuba za su bude ofishin jekadancinsu

Kungiyar Kasashen Turai ta yaba da abin tarihin da tace an yi wajen mayar da huldar jakadanci tsakanin Amurka da cuba bayan shafe shekaru 54 kasashen na takun-saka.

An shafe shekaru 54 kasashen Amurka da Cuba na takun-saka.
An shafe shekaru 54 kasashen Amurka da Cuba na takun-saka. RFI/Silvia Chocarro
Talla

A jiya Laraba Cuba da Amurka sun amince su farfado da huldar diflomasiya tsakaninsu, tare da sake bude ofishin jekadancinsu a Havana da Washington.

Kungiyar Turai ta sanar da matsayinta bayan kasashen biyu sun sanar da kawo karshen rashin jituwar da ke tsakaninsu.

Dangane da katse takunkumin kasuwanci kuma da aka yi tun shekarar 1962, kungiyar kasashen Turai ta bayyani shi a matsayin abin bakin ciki wanda ya kamata a kawo karshen sa.

Kungiyar ta bukaci Amurka da cuba su ci gaba da tattaunawa don warware duk wata takaddama ko shinge da ke tsakanunsu domin haifar da ci gaba da kuma dangantaka mai kyau.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.