Isa ga babban shafi
Amurka-Cuba

Amurka da Cuba sun sasanta da juna

Amurka da Cuba sun farfado da huldar diflomasiyarsu a hukumance a yau Litinin bayan sun shafe shekaru 50 suna wa juna kallon hadarin kaji. Kasashen biyu za su bude ofishin jekadancinsu a Havana da Washington.

Shugaban Amurka Barack Obama da Raul Castro na Cuba
Shugaban Amurka Barack Obama da Raul Castro na Cuba REUTERS/Kai Pfaffenbach
Talla

Kasashen biyu za su daga tutocinsu a ofishin jakadacinsu a Havana da Washington, wanda shi ne karon farko tun cikin shekarar 1961.

Amma sai an yi gyaran ginin da zai zama ofishin jakadancin kasar Amurka a birnin Havana na kasar Cuba.

Ana sa ran a yau Litinin Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry zai gana da takawaransa na Cuba Bruno Rodriguez.

Tun a watan Disemba ne kasashen biyu suka amince su sasanta da juna, bayan shugaban Amurka Barack Obama da Raul Castro sun amince su kawo karshen takun sakar da ke tsakaninsu.

Sasantawar kasashen biyu dai zai taimaka wajen farfado da tattalin arzikin Cuba, idan har Amurka ta janye takunkumin da ta kakabawa kasar tun a 1960.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.