Isa ga babban shafi
Turai-Cuba-Amruka

kasashen turai na kokarin kyautata huldarsu da Cuba da wasu kasashen latin Amruka

Shuwagabannin Kasashen Turai sun sha alwashin kamala tattaunawa da kasar Cuba, dan mayar da huldar diflomasiya tare da baiwa Colombia kudade idan an samun zaman lafiya a kasar.

Ministocin Faransa da Cuba na sanya hannu kan kulla sabuwar hulda
Ministocin Faransa da Cuba na sanya hannu kan kulla sabuwar hulda REUTERS/Yamil Lage
Talla

Shugabanin kasashe 28 dake kungiyar EU sun kuma bayayna shirin zuba jari da kuma tattaunawa da kasashen Yankin Latin Amurka 33 da na Carribean.

Shugaban Majalisar Turai Donald Tusk ya bayyana goyan bayansa kan tattaunawar da ake yi da Cuban, bayan ya bayyana farin cikinsa da Makamancin irin wannan matakin da Amurka ta dauka.

Tusk ya kuma ce, kungiyar zata kafa wata gidauniya dan tallafawa Colombia, wajen sake gina kasar, bayan an kulla yarjejeniyar zaman lafiya da Yan Tawayen FARC.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.