Isa ga babban shafi
Ukraine

Alamu na tabbatar da harbo jirgin Malaysia aka yi a Ukraine

Masu bimcike da ke nazarin yadda aka harbo jirgin saman kasar Malaysia mai lamba MH17, sun ce da alama harbo jirgin aka yi da makamin Roka samfurin BUK da aka kera a kasar Rasha.

Ana zargin 'Yan tawayen Ukraine ne suka harbo Jirgin Malaysia MH17
Ana zargin 'Yan tawayen Ukraine ne suka harbo Jirgin Malaysia MH17 REUTERS
Talla

Masu binciken sun ga alamun haka ne yayin da suke nazarin inda lamarin ya faru a gabashin kasar Ukraine, inda jirgin ya fado.

Masu binciken da suka fito daga kasar Netherlands, da sauran kasashen duniya, suna nazarin sassan makamin ne, wanda alamu ke nuna cewa samfurin BUK ne, da ake cilla daga kasa zuwa sararin samaniya.

Sanarwar da masu binciken laifukan suka fitar ta ce tun lokacin da aka yi bincike baya, aka adana sassan makamin a hukumar kiyaye hadurra ta kasar Holland.

Ranar 17 ga watan Yulin bara, aka harbo jirgin na kasar Malaysia, mai lamba MH17 lokacin da ya ke keta sararin samaniyan kasar Ukraine, dauke da mutane 298.

Lamarin dai ya faru ne lokacin da ake bata-kashi tsakanin dakarun kasar Ukraine da ‘yan awaren da ke samun goyon bayan kasar Rasha.

Tun a lokacin mahukuntan birnin Kiev, da sauran kasashen yammacin duniya ke zargin ‘yan tawayen da amfani da makamin kirar kasar Rasha wajen harbo jirgin, zargin da kuma mahukuntan birnin Moscow da ‘yan tawayen ke musantawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.