Hukumomi a Afghanistan Sun ce Mutane 51 Suka Mutu a Hare-Haren Bama-Bamai na Juma'a
Hukumomi a kasar Afghanistan sun gaskata cewa mutane 51 ne suka mutu bayan kazaman hare-haren bama-bamai ranar Juma'a a birnin Kabul mafi muni tun bayan ficewar dakarun kawance na hadin guiwa na NATO a watan 12 da ya gabata.
Wallafawa ranar:
Harin na jiya ya lalata gine-gine da yawa da jikkata daruruwan mutane.
Asibitoci sun cika sun batse da mutane da suka sami raunuka yayin hare-haren mafiya muni tun bayan sanar da mutuwar Shugaban Taliban Mullah Omar.
Hare-haren na kara nuna rashin tabbacin ingantaccen tsaro a wannan kasa da yaki ya lalata.
Harin farko cikin dare ranar Juma'a a tsakiyar birnin Kabul mutane 15 suka mutu nan take , yayinda wasu 250 suka jikkata.
Daga bisani kuma aka sake samu wani hari a harabar inda ake daukan kuratan 'yan sanda inda nan take kurata da wasu fararen hula 27 suka mutu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu