Isa ga babban shafi
Afghanistan

Shugaban Taliban ya halatta tattaunawarsu da Afghanistan

Shugaban Kungiyar Taliban Mullah Omar ya halaccin taron sasantawa tsakaninsu da wakilan gwamnatin kasar Afghanistan amma ba tare da yin Karin bayani akai ba

Mayakan Taliban sun shafe shekaru 13 suna yaki a Afghanistan
Mayakan Taliban sun shafe shekaru 13 suna yaki a Afghanistan REUTERS
Talla

A sakon da ya aikewa magoya bayansa na Sallar Eid el Fitr, Mullah Omar ya ce tattaunawar na da muhimmanci muddin za ta kawo karshen mamayar da kasahsen Yammacin duniya suka yi wa kasar.

A makon jiya aka fara tattaunawa tsakanin gwamnatin Afghanistan da kungiyar Taliban a kasar Pakistan.

Kuma bangarorin biyu sun amince su ci gaba da tattaunawa bayan kamala azumin Ramadan domin cim ma yarjejeniyar samar da zaman lafiya a Afghanistan.

Tuni dai kungiyar Tsaro ta NATO ta kawo karshen ayyukanta a Afghanistan bayan shafe shekaru dakarun Kungiyar na fada da mayakan Taliban.

Sojojin Kasar Pakistan sun bayyana aniyarsu na ganin gwamnatin Afghanistan ta kulla yarjejeniyar zaman lafiya da kungiyar Taliban a taron da suke gudanarwa yanzu haka a kasar.

Majiyar sojin kasar tace wannan yunkurin da aka fara ganawa ranar 8 ga wata a Islambad ya tabbatar da aniyar Pakistan na ganin an kawo karshen tashin hankalin da ya hallaka dubban rayukan jama’a.

An dade ana zargin Pakistan da taimakawa Taliban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.