Taliban ta kai harin farko a Afghanistan bayan mutuwar shugabanta
Kungiyar Taliban ta hallaka mutane 6 a harin farko da ta kai Cibiyar jami’an tsaro a Afghanistan bayan sauyin shugabancin da aka samu a kungiyar sakamakon rasuwar Mullah Omar.
Wallafawa ranar:
Mataimakin jami’in Yan Sandan Afghanistan da ke Yankin Logar Muhammad Qari Wara ya ce wata motar tankin ruwa shake da bama bamai ne ta fashe inda ta kashe fararen hula uku da jami’an tsaro uku.
Ma’aikatar cikin gidan kasar ta tabbatar da harin wanda shi ne na farko da Mayakan Taliban suka yi ikirarin kai wa tun bayan mutuwar shugabansu Mullah Umar.
A ranar Juma’a ne Taliban ta sanar da nada Mullah Akhtar Mansour a matsayin sabon shugaba.
A cikin makon nan ne wani rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya bayyana cewa an samu karuwar mutuwar fararen hula a kasar Afghanistan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu