Isa ga babban shafi
FIFA

Switzerland ta zurfafa bincike akan FIFA

Masu gabatar da kara a kasar Switzerland sun ce Zarge zargen cin hanci da rashawa da almundahana da ake zargin Jami’an hukumar FIFA sun kai 81 sabanin 53. Kuma zarge zargen sun shafi batun ba Qatar da Rasha damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya.

Manyan Jami'an FIFa da dama ne ake zargi sun karbi cin hanci domin ba Qatar da Rasha damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya
Manyan Jami'an FIFa da dama ne ake zargi sun karbi cin hanci domin ba Qatar da Rasha damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya REUTERS/Ruben Sprich/Files
Talla

Hukumomin Shari’a a Switzerland sun bankado wasu karin zarge-zarge da ake tuhumar jami’an hukumar FIFA kan badakalar ba Qatar da Rasha damar daukar nauyin gasar cin kofin duniya a shekaraar 2018 da 22.

Masu gabatar da kara a kasar sun ce zarge zagen sun kai 81 sabanin 53 da babban alkalin alkalan kasar ya bayyana a farko.

Dukkanin zarge zargen sun shafi batun ba Qatar da Rasha damar karbar gasar cin kofin duniya.

Yanzu haka kuma mahukunatan na Switzerland sun rufe asusun ajiyar kudaden cin hanci amma ba su bayyana adadin kudaden ba.

Kuma mahukuntan sun kafa kwamiti na musamman domin binciken ba Qatar da Rasha damar karbar bakuncin gasar cin kofin duniya.

A watan jiya ne dai mahukunatan Amurka suka caji jami’an hukumar FIFA 14 da laifukan da suka shafi cin hanci, kuma yanzu haka suna kan ci gaba da bincike inda wasu ke ganin har da shugaban hukumar ta FIFA Sepp Blatter ba zai sha ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.