Isa ga babban shafi
FIFA

Blatter ya ki yin murabus

Sepp Blatter ya yi watsi da bukatar Majalisar Dokokin Tarayyar Turai wacce ta bukaci shugaban hukumar kwallon kafan duniya FIFA ya gaggauta sauka daga mukaminsa, domin bayar da damar nada shugaba na riko da zai soma aiwatar da sauye-sauye a hukumar.

Shugaban FIFA Joseph Blatter
Shugaban FIFA Joseph Blatter REUTERS/Ruben Sprich
Talla

Majalisar da ke birnin Strasbourg na Faransa, ta ce saukar Blatter a cikin gaggauwa ita ce za ta kawo kwanciyar hankali a hukuma da ke da alhakin tafiyar da harkar kwallon kafa a duniya.

A ranar biyu ga watan Yuni ne Blatter mai shekaru 79 ya sanar da cewa zai yi murabus daga mukaminsa, amma ya ce sai a watan Disamba zai ajiye aikinasa inda za a zabi sabon shugaba.

Sai dai kuma kakakin hukumar FIFA ya ce hankalin Blatter ya karkata ga tabbatar sabbin sauye sauye kafin ya ajiye mukaminsa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.