Isa ga babban shafi
FIFA

Ban yi murabus ba- Blatter

Shugaban hukumar FIFA Sepp Blatter ya yi ikirarin cewa bai yi murabus ba a matsayin shugaban hukumar da ke kula da kwallon kafa a duniya, kamar yadda ya shaidawa wata Jarida kasar Switzerland.

Sepp Blatter Shugaban FIFA
Sepp Blatter Shugaban FIFA REUTERS/Arnd Wiegmann
Talla

Jaridar Blick ta ce Blatter ya shaida ma ta cewa yana nan kan mukaminsa har sai babban taron hukumar ya tantance makomarsa.

A ranar 2 ga watan Yuni ne Blatter ya bayyana cewa zai yi murabus a wani babban taron hukumar FIFA na musamman da za a gudanar a watan Disemban bana. Wannan kuma na zuwa ne sakamakon cafke wasu manyan jami’an FIFA kan zargin rashawa da ya dabaibaye hukumar.

Kwamitin Zartarwar FIFA dai zai gana a ranar 20 ga watan Yuli a birnin Zurich inda ake sa ran za a tsayar da ranar da za a zabi wanda zai gaji Blatter.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.