Isa ga babban shafi
Iran

Manyan kasashen duniya sun zarce wa’adin tattaunawarsu da Iran

Wakilan Kasashen duniya da ke tattaunawa da Iran kan shirinta na mallakar makaman nukiliya sun ce ya zama dole a kammala tattaunawar cikin sa’oi 48 ma su zuwa bayan sun kasa kulla yarjejeniya daren Talata da wa’adin tattaunawarsu ya kawo karshe.

Zauren tattauna batun nukiliyar Iran a Vienna
Zauren tattauna batun nukiliyar Iran a Vienna Reuters
Talla

Manyan kasashen sun ce ba zasu dauki wani dogon lokaci suna tattaunawar da taki karewa ba, a dai dai lokacin da Iran ta nuna rashin amincewar ta kan tsawaita hana ta cinikin makamai.

Majalisar Dinkin Duniya tace takunkumin cinikin makamai da aka sanya wa hukumomin birnin Tehran zai kasance cikin kudurin yarjejeniyar.

Kasashe bakwai da ke tattauna batun sun tabatar da cewa ba za su kawo karshen tattaunawar ba kamar yadda aka tsara, sai dai kuma sun nemi karin ‘yan kawanaki don a samu kai wa ga kulla yarjejeniyar da za ta taimaka wajen hana Iran kera makaman Nukiliya.

Masu shiga tsakani suna daukar batutuwan da ke kunshe cikin yarjeniyoyin daki-daki, tare da hada muhimman batutuwan da ke cikin tattaunawar da aka shafe kusan shekaru biyu ana yi.

Wani jami’in gwamnatin Amurka ya ce ba a taba kawo wa irin matakin da ake ba a yanzu, kuma har yanzu ana ci gaba da kokarin ganin an cim ma matsaya kan batun.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.