Isa ga babban shafi
Iran

Mun kusan cim ma yarjejeniya da Iran- Kerry

Sakataren harakokin wajen Amurka john Kerry ya ce akwai yiyuwar za su cim ma yarjejeniya da Iran kan shirinta na mallakar makaman Nukiliya amma akwai batutuwa da dama da suke da sabanin ra’ayi.

Sakataren wajen Amurka  John Kerry
Sakataren wajen Amurka John Kerry REUTERS/Carlos Barria
Talla

A gobe Talata ne ake sa ran kammala tattaunawa tsakanin wakilan manyan kasashen duniya guda 6 da kuma Iran kan shirinta na nukiliya. John Kerry ya ce har yanzu akwai batutuwan da ke da sarkakiya tsakaninsu.

Amma ministan harakokin wajen Iran ya yi watsi da ikirarin na Kerry, yana mai cewa sabanin da ke tsakaninsu ba zai sa su cim ma yarjejeniya ba.

John Kerry da ke jawabi ga manema labarai a Vienna ya ce lokaci ya yi da za su dinke barakar da ke tsakaninsu kan batutuwan da har yanzu kowanne bangare ke dogewa akai.

Kerry ya ce sun samu ci gaba a kwanakin da suka wuce, sai dai har yanzu akwai batutuwa masu muhimmanci da kowanne bangare ya tsaya kai da fata.

Kerry wanda ya kwashe dogon lokaci yana ganawa da takwaransa na iran Mohammed Javad Zarif, kafin isar ministocin kasashen Rasha da Birtaniya da Faransa da Jamus da China, ya ce duk da ci gaban da suka samu tattaunawar na iya samun nasara a cikin makon nan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.