Yarjejeniyar Shirin Nukiliyar Iran na gab da Nasara
Ministan harkokin wajen Iran Muhammad Javad Zarif, ya shaida cewa an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar da ake yi game da shirin nukiliyar kasar a birnin Vienna. To sai dai akwai bukatar sadaukarwa daga kowane bangare kafin cimma yarjejena kan wannan batu.
Wallafawa ranar:
Javad Zarif ya ce akwai sauran ‘yan bambance-bambancen da suka rage a tsakaninsu, sai dai kuma yana ganin cewa ba su taba kusantar matsayi na fahimtar juna kamar yadda sukayi a jiya ba, to amma duk da haka ba shi da tabbas, saboda kafin cimma yarjejeniya, akwai bukatar sadaukarwa daga kowane bangare.
Ya kuma bayyana yadda wasu da farko suka bukaci yin amfani da karfin soja da takunkumai na tattalin arziki domin tursasawa Iran, amma daga karshen suka rungumi hanyar tattaunawa, to amma duk da haka, a akwai bukatar yin wani abu da za a bayyana shi a matsayin tarihi, ina nufin cimma yarjejeniya a cewar Ministan.
Iran dai na cewa anata bangare ta shirye domin kulla yarjejeniyar da babu kwaruwa a cikinta, domin buda sabon babi da nufin fuskantar muhimman kalubale da ke gabansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu