Isa ga babban shafi
Amurka

Amurkawa na bikin ranar 'yancin-kai a cikin fargaba

Hukumomi a kasar Amurka sun tsananta matakan tsaro a yau asabar a daidai lokacin da kasar ke gudanar da bukukuwan ranar ‘yancin-kai, sakamakon karuwar barazanar ayyukan ta’addanci a duniya.

Jami'an FBI na kokarin kwace wata nakiya
Jami'an FBI na kokarin kwace wata nakiya REUTERS/Jeremy Papasso
Talla

Hukumar tsaron cikin gidan kasar ta Amurka da kuma hukumar yaki da ayyukan ta’addanci ta kasar, sun ce akwai karuwar barazana daga ‘yan ta’adda, musamman ma a wannan lokaci da Amurka ke gudanar da bukukuwan zagayowar ranar ‘yancin-kai.

Gwamnan New York Andrew Cuoma, ya ce birnin na daga cikin wadanda suka fi fuskantar barazana daga ‘yan ta’addar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.