Isa ga babban shafi
Amurka

Wata bakar fata ta cire tutar wariyar launin fata a Amurka

A Kasar Amurka, Wata mata bakar fata mai suna Bree Newsome ta cire tutar dake nuna wariyar launin fata da aka kafa a gidan gwamanti dake jihar kudancin Carolina. 

Matar da ta cire tutar a hannun jami'an 'Yan Sandan Amurka
Matar da ta cire tutar a hannun jami'an 'Yan Sandan Amurka lovebscott.com
Talla

Tuni dai hukumomi suka cafke Newsome bayan ta sauko daga inda aka kafa tutar.

Ana ta yada hotunan Newsome mai sekaru 30 a shafukan sada zumunta, inda aka nuna ta a hannun hukuma kuma tuni aka mayar da tutar bagirenta.

Wannan dai na zuwa ne bayan wani matashi farar fata mai suna Dylaan Roof ya harbe har lahira bakaken fata 9 dake ibada a wata mujami’a dake kudancin Carolina na Amurka.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.