Isa ga babban shafi
UNESCO

UNESCO ta soki Saudiya akan rusa kayan Tarihi a Sanaa

Hukumar UNESCO da ke raya al’adu da ilimi da kimiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta nunu damuwarta tare da kalubalantar kasar Saudiya, dangane da yadda hare-haren da ta ke kai wa a kasar Yemen ke lalata kayayyakin tarihin kasar, musamma a tsohon birnin Sana’a.

Garin Sanaa da hare haren Saudiya da kawayenta suka ruguza a Yemen
Garin Sanaa da hare haren Saudiya da kawayenta suka ruguza a Yemen REUTERS/Khaled Abdullah
Talla

UNESCO ta bukaci, a dai na ruguza kayayyakin tarihin da sunan yaki.

Darakta Janar, ta UNESCO Irina Bokova, ta ce harin bama-bamai da Saudiya da kawayenta ke kai wa kan ‘yan tawayen Yemen ya lalata yawanci dadaddun kayayyakin tarihin kasar, da kasashen Larabawa ke alfahari da su.

Irina ta ce akwai gine-gine a birnin Yemen, da kuma tsohon wajen ajiyar kayayyaki tarihi na Saada, da bangon tarihin Islama na Baraqish da duk hare-hare bama-bamai ya rugurguza.

UNESCO ta bayyana damuwarta dangane da yadda hare-haren suka shafi abubuwan tarihi wanda ke bada labarin asalin ‘yan kasa, da kuma hidimar da kaka da kakanni suka yi kafin zuwan Musulunci.

Tsohon Birnin Sanaa da ke cikin wasu tsaunika, Gari ne da aka kafa sama da shekaru dubu 2500, kuma ana ganinsa a matsayin cibiyar musulunci. Mai dauke da masallatai fiye da 100 da kuma wasu gidaje sama da dubu shida da aka gina tun karni na 11.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.