Isa ga babban shafi
Yemen

Saudiya ta tarwatsa cibiyar aje makamai a Yemen

Hukumomin kiwon lafiya a birnin Sanaa na kasar Yemen sun tabbatar da mutuwar mutuwar mutane 69 sakamakon harin da sojojin kawancen Saudiya suka kai akan wani rumbun ajiye makamai da ke birnin. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da shirin tsagaita wuta tsakanin ‘yan tawayen Houthi da kuma sojojin kawance a karkashin jagorancin Saudiya ke fara aiki a yau Talata.

An kashe daruruwan mutane a Yemen.
An kashe daruruwan mutane a Yemen. REUTERS/Mohamed al-Sayaghi
Talla

Ma’aikatar kiwon lafiyar kasar ta Yemen ta ce mafi yawa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan hari fararen hula ne, yayin da wasu akalla 250 suka samu raunuka.

Da misalin karfe 8 na daren yau agogon GMT ne ya kamata yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwanaki biyar da aka cim ma tsakanin bangarorin biyu za ta fara aiki, domin bai wa jami’an agaji damar raba kayayyakin abinci da magunguna ga mutane kusan milyan biyu da ke cikin mawuyacin hali.

Mai magana da yawun hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya Elizabeth Byrs, ta ce kawo yanzu hukumarta na cikin shirin bai wa mutane dubu 750 abinci a sassa daban daban na kasar.

A yau ne dai sabon manzon Majalisar Dinkin Duniya a kasar Yemen Isma’il Ould Shekh Ahmed dan asalin kasar Mauritania ya isa birnin Sana’a domin fara aiki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.