Isa ga babban shafi

Shugaba Rousseff ta lashi takobin yaki da cin hanci a Brazil

Shugabar Kasar Brazil, Dilma Rousseff, ta sanar da shirinta na yaki da cin hanci, bayan badakalar cin hanci da tayi awon gaba da jiga jigan jam’iyyarta a yanzu.Dilma Rousseff ta sanar da shirin nata ne, bayan badakalar cin hancin a ma’aikatar man Kasar, na Petrobras da kuma ake zargin wasu jiga jikan jam’iyyarta dashi.Rousseff ta bayyana cewa, gwamnatin ta ba zata amince da cin hancin da rashawa ba, yayinda ta jaddada kudirin gwamnatin na hukunta masu tunanin sunfi karfin doka.Yanzu haka dai, shirin zai kunshi kwace kayyakin da ‘yan siyasa suka mallaka, amma suka kasa da bada cikakkun bayanai kan yadda suka same su.Kana za’a dakatar da duk wani jami’in gwamnati da aka taba samun sa da babban laifi.A karshen makon daya gabata ne, ‘yan kasar ta Brazil su kimanin miliyon daya da rabi, suka gudanar da zanga zanga a titinan kasar, inda suka soki gwamnatin Rousseff, yayinda a yanzu kuma akwai kimanin ‘yan siyasa 50 dake fuskantar tuhuma kuma akasarinsu nada kayyawar alaka da shugabar. 

La presidenta Dima Rousseff durante la ceremonia de anuncio de las medidas contra la corrupción en Brasilia, 18 de marzo de 2015.
La presidenta Dima Rousseff durante la ceremonia de anuncio de las medidas contra la corrupción en Brasilia, 18 de marzo de 2015. REUTERS/Ueslei Marcelino
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.