Isa ga babban shafi
Brazil

Ana ci gaba da zanga zangar adawa da Dilma Rousseff a Brazil

A kalla mutane miliyan daya da rabi ne suka shiga wata zanga zangar adawa da gwamnatin shugaba Dilma Rousseff ta Brazil saboda matsalar tattalin arziki da kuma zargin cin hancin da ya dabaibaye kanfanin man fetur din kasar.Masu zanga zangar sun bukaci majalisar kasar da su tsige shugabar kasar wadda ke kasa da watanni shida kan karagar mulki wa’adi na biyu a zaben da ya raba kan al’ummar kasar.An dai gudanar da zanga zanga mafi girma ne a Sao Paulo babban birnin kasuwancin kasar, inda aka ce mutane sama da miliyan daya suka shiga sanye da kayan dake nuna tutar kasar.Rahotanni sun ce an gudanar da zanga zangar a garuruwa 83 a fadin kasar. 

Brazil's President Dilma Rousseff reacts during a meeting with International Olympic Committee (IOC) President Thomas Bach (not pictured) at the Planalto Palace in Brasilia, July 11, 2014.
Brazil's President Dilma Rousseff reacts during a meeting with International Olympic Committee (IOC) President Thomas Bach (not pictured) at the Planalto Palace in Brasilia, July 11, 2014. Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.