Isa ga babban shafi
Brazil-FIFA

Rousseff ta gana da bangarorin siyasar Brazil

Shugabar kasar Brazil Dilma Russeff wadda kasarta ke fuskantar mummunar tarzoma sakamakon tsadar rayuwa, yanzu haka tana ci gaba da ganawa da bangarorin siyasa da na al’ummar kasar domin sanar da su shirinta na gudanar da kuri’ar raba gardama da nufin kawo karshen rikicin kasar.

Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff
Shugabar kasar Brazil Dilma Rousseff Reuters / Marcelino
Talla

A nasa bangaren, Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA Joseph Blatter, wanda ke kasar domin halartar gasar karshe ta cin kofin kwallon kafa na Zakarun nahiyoyin duniya, ya ce ya fahinci dalilan da suka haddasa wannan zanga-zangar na kashe makuddan kudade wajen shirya wasanni, amma a cewarsa ba abin da hukumarsa za ta iya yi dangane da haka.

Blatter yace duk da ana gudanar da wasannin ne cikin fargaba saboda masu zanga-zanga amma an a ganinsa an gudanar da wasannin cikin lumana da kwanciyar hankali.

Wannan zanga-zangar dai ita ce mafi muni cikin shekaru 20 da aka taba gani a kasar Brazil.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.