Isa ga babban shafi
MDD

Kasashen duniya sun amince da hanyoyin rage dumamar yanayi

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-Moon, ya yaba da yadda kasashen duniya suka sanya hannu kan yarjejeniyar rage dumamar yanayi a taron canjin yanayi da aka kammala a birnin Lima na kasar Peru, tare da yin kira ga manyan kasashen duniya su aiwatar da yarjejeniyar kafin taron Paris a badi. Yayin taron, kasashen dake da wakilici Majalisar Dinkin Duniya, sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar yaki da matsalar, ta hanyar rage gurbataccen hayakin da suke fitarwa domin kawo karshen dumamar yanayi a duniya.Sakararen Janar na Majalisar ta Dinkin Duniya Ban Ki-moon, ya yaba da matakin, tare da yin kira ga manyan kasashe masu yawan masana’antu su aiwatar da yarjejeniyar.Wannan kuma ya bude kofar amincewa da yarjejeniyar ne a taron Paris da za’a gudanar a shekara mai kamawa.Matsalar canjin yanayi dai na ci gaba da zama barazana a duniya, akan haka ne Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranci taro a Lima, don tattauna hanyoyin da za a magance matsalar.Babban batun da kuma ake jayayya a kai, shine yadda manyan kasashe masu yawan masana’antu zasu biya kananan kasashe diya, sakamakon yadda dumamar yanayin ke yi musu illa.Ana dai bukatar kasashen su tsaya kan iya yawan hayakin da aka takaita masu su fitar a sararin samaniya, don kawo karshen matsalar dumamar yanayi daga nan zuwa shekarar 2020. 

Le secrétaire général des Nations Ban Ki-moon, le 12 octobre 2014, au caire.
Le secrétaire général des Nations Ban Ki-moon, le 12 octobre 2014, au caire. REUTERS/Mohamed Abd El Ghany
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.