Isa ga babban shafi
Saudi-Amurka

Kasashen Larabawa sun aminta da tsarin Amurka akan IS

Gungun kasashen Larabawa sun goyi bayan matakin shugaban Amurka Barack Obama na fadada farmaki akan Mayakan IS da suka mamaye yankuna a kasashen Iraqi da Syria, bayan sun kammala taro da John Kerry a Jeddah. Amma Gwamnatin Syria ta yi wa kasashen kashedi.

Ministocin harakokin wajen kasashen Larabawa tare da Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry
Ministocin harakokin wajen kasashen Larabawa tare da Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry Reuters
Talla

Gungun kasashen Larabawa guda 10, karkashin jagorancin Saudiya sun amince su yi wa Mayakan IS taron dangi wadanda ke gwagwarmayar shinfida sabuwar daula bayan sun mamaye wasu yankuna a Syria da Iraqi.

Kasashen na larabawa sun amince da matakin ne bayan sun tattauna da Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry a birnin Jeddah na Saudiya.

‘Yan tawayen Syria da sabuwar gwamnatin hadin kai a Iraqi sun yi na’am da tsarin fattakar mayakan na IS da Amurka ta shinfida, amma Gwamnatin Bashar al Assad a Syria da Rasha sun kalubalanci matakin.

Syria ta yi kashedin cewa duk wani mataki da aka dauka, ba tare da tuntubarta ba, tamkar hari ne aka kaddamar akanta.

Rasha ma aminiyar Syria ta gargadi Amurka, tana mai cewa matakin ya keta dokokin duniya.

A ranar Laraba ne shugaban Amurka Barack Obama yace zai aika da wasu tawagar kwararrun Sojoji kusan 500 domin bayar da horo ga Sojojin Iraqi, kuma Amurka zata hada hannu ne da ‘Yan tawayen Syria da kuma mayakan sa-kai Kurdawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.