Iraqi-Amurka
Amurka ta nemi a hade kai wajen yakar kungiyar IS
Amurka ta shata hanyoyin da gamayyar kasashen duniya zasu bi, don samun galaba kan mayakan kungiyar IS a kasashen Iraq da Syria. Lokacin da yake jawabi a wajen taron kungiyar tsaro ta NATO, Shugaba Barak Obama yace Amurka zata yi kokarin samun hadin kan kawayenta na yankin gabas ta tsakiya, don samun nasara kan mayakan jihadin.Shugaban yace yana da matukar muhimmanci a shigar da kasashen yankin a wannan kokarin, sai dai ma’aikatar harkokin wajen Amurkan tace kasar bata tunannin shigar da Iran cikin wannan aikin.
Wallafawa ranar: Chanzawa ranar: