Isa ga babban shafi
Rasha

Rasha ta tsara sabbin takunkumi akan Turai da Amurka

Kasar Rasha ta tsara sabbin takunkumin da zata kakaba akan kasashen Turai da Amurka da suka hada da haramta shigo da motocin da aka yi amfani da su bayan kasashen na yammaci sun amince su tsaurara wa Moscow takunkumi saboda rikicin Ukraine.

Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin
Shugaban kasar Rasha, Vladimir Putin REUTERS/B.Rentsendorj
Talla

Kamfanin Dillacin labaran Rasha ya ruwaito wani na hannun damar shugaban kasar Vladimir Putin yana cewa bangaren ci gaban tattalin arzikin kasar ya tsara sabbin takunkumi akan kasashen yammaci.

Andrei Belousov yace akwai wasu kayyakin da ba su shafi abinci ba da kasashen yammaci ke dogaro da Rasha wadanda suka hada da motocin da aka yi amfani da su da tufafi.

Kasar Rasha tace tana iya dogaro da kanta ba lalle sai ta dogara da kasashen na Turai ba.

A ranar Juma’a ne kasashen Turai suka amince su tsaurarawa kasar Rasha takunkumi saboda ruwa da tsaki da kasar ke yi a rikicin Ukraine.

A watan jiya ne kuma Rasha ta haramta shigo da kayan abinci daga Amurka da kasashen Turai domin mayar da martani ga takunkumin da suka kakaba ma ta tun da farko.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.