Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Isra’ila na ci gaba da luguden wuta a Gaza

Sojojin Isra’ila sun kashe Falasdinawa akalla shida a farmakin da suke ci gaba da kai wa ta jiragen sama a Gaza. Kungiyar Hamas ta falasdinawa tace Isra’ila ta kashe kwamnadojinta uku a hare haren da ta kai a Rafa da sanyin safiyar Alhamis.

Falasdinawa na aikin tono gawawwaki a benen da hare haren Isra'ila suka tarwatsa a Gaza.
Falasdinawa na aikin tono gawawwaki a benen da hare haren Isra'ila suka tarwatsa a Gaza. Reuters
Talla

Kungiyar da ke kula da ayyukan jin kai a Gaza ta tabbatar da mutuwar mutane shida, kuma hudu daga cikinsu yara kanana ne a hare haren da Isra’ila ta kai a Gaza da kuma Bait Lahiya.

Kungiyar Hamas ta falasdinawa tace Isra'ila ta kashe kwamnadojinta uku a hare haren da ta kai Rafa yau da asuba. Bangaren Sojin kungiyar da ake kira Ezzedine al Wassam Brigade ya sanar da kwamandojin da aka kashe da suka hada da Mohammad Abu Shamala da Raed al Atar da Mohammed barhum.

Shaidun gani da ido sun ce harin na yau da safe ya rusa wani bene mai hawa 4 inda ya kashe mutane 7.

Tun kaddamar da sabon rikici tsakanin Isra’ila da Hamas a ranar 8 ga watan Yuli, Yahudawa 67 suka mutu amma akalla yanzu Falasdinawa 2,058 Isra’ila ta kashe.

Sabbin hare haren na zuwa ne bayan Hamas ta sanar da katse tattaunawar samun zaman lafiya tsakaninta da Isra’ila, tare da yin gargadi ga kamfanonin jiragen sama da su kaucewa zuwa Tel Aviv saboda hare haren da za ta kaddamar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.