Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Gaza: Yarjejeniyar tsagaita wuta ta kawo karshe

A yau Juma’a yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki uku, tsakanin Isra’ila da Hamas ta kawo karshe a Gaza, ba tare da bangarorin biyu sun amince a tsawaita yarjejeniyar ba. Rundunar Sojin Isra’ila ta ce Mayakan Hamas sun harba rokoki bayan wa’adin yarjejeniyar tsagaita wutar ya kawo karshe.

Gidan Shugaban Kungiyar Hamas Isma'il Haniya da Isra'ila ta tarwatsa a Gaza.
Gidan Shugaban Kungiyar Hamas Isma'il Haniya da Isra'ila ta tarwatsa a Gaza. REUTERS/Finbarr O'Reilly
Talla

Yarjejeniyar tsagaita wuta ta sa’o’I 72 ta kawo karshe da Isra’ila da Hamas suka amince, a yayin da suke ci gaba da tattaunawa a birnin Al Kahira.

Amma bayan cikar wa’adin yarjejeniyar, rundunar Sojin Isra’ila tace Mayakan Hamas sun harba rokoki zuwa cikin Isra’ila daga zirin Gaza, bayan Hamas da dukkanin bangarorin Falasdinawa sun yi watsi da matakin tsawaita yarejejeniyar tsagaita wutar.

A cikin wata sanarwa, Sojin Isra’ila tace Hamas ta cilla rokoki akalla guda biyar da asubahin Juma’a zuwa kudancin Isra’ila. Kodayake wasu ‘Yan gwagwarmaya da ake kira Al Quds Brigade sun ce su suka harba rokoki uku zuwa Isra’ila.

Hamas dai ta ki amincewa a tsawaita yarjejeniyar tsagaita wuta, saboda Isra’ila ta ki amincewa da bukatun Falasdinawa.

Tsawon wata guda dai aka kwashe ana zubar da jini a Gaza, tsakanin Isra’ila da Hamas, rikicin da ya hallaka Falasdinawa 1,890, yawancinsu fararen hula, yayin da kuma aka kashe Sojojin Isra’ila 67.

Yanzu haka Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya umurci Sojojin Isra’ila su kaddamar da hari a Gaza domin mayar da martani ga hare haren rokoki da ake zargin Mayakan Hamas sun cilla a kudancin kasar bayan wa’adin yarjejeniyar tsagaita wuta ta kwanaki uku ta kawo karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.