Isra’ila da Hamas sun koma teburin sulhu
Wakilan Isra’ila da Hamas sun soma tattaunawa a kasar Masar domin cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta mai dorewa, kafin wa’adin ta wuccin gadi ya cika, da nufin kawo karshen zubar da jini a Gaza.
Wallafawa ranar:
Kusan Falasdinawa 2,000 Isra’ila ta kashe sama da wata guda tana kai farmaki a Gaza
Kasar Masar da ke jagorantar zaman tattautawar, tana fatar bangarorin biyu zasu amince da sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta.
Kodayake wakilan Hamas suna da bukatu da suke son dole sai Isra’ila ta amince kafin su amince da yarjejeniyar, musamman bukatar neman a kawo karshen killacewar da Isra’ila ta yi wa zirin Gaza tsawon shekaru bakwai.
Isra’ila kuma tana da bukatu na tsaro da ta ke son Hamas ta amince kafin kulla sabuwar yarjejeniyar ta tsagaita wuta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu