Isa ga babban shafi
Isra'ila-Hamas

Sabon shirin tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra'ila

Babban jami’in hukumar kula da ayyukan jinkai na Majalisar Dinkin Duniya James W. Rawley, ya ce duk wani yunkuri domin samar da yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da Hamas ba zai yi tasiri ba matukar dai aka bar Isra’ila na ci gaba da killace zirin Gaza.

Sojan Isra'ila na janyewa daga Gaza
Sojan Isra'ila na janyewa daga Gaza REUTERS/Nir Elias
Talla

Rawley ya bayyana cewa alhaki ya ratawa a wuyan kasashen duniya domin ganin cewa Isra’ila ta kawo karshen killance Gaza wanda a yau ya share tsawon shekaru 7.

Har ila yau jami’in na MDD ya yi kakkausar suka a game da yadda kasashen duniya suka zura ido har aka samu asarar rayukan Falasdinawa 1,930 da kuma wasu Yahudawa 67 a cikin makonni 4 da aka share ana gwabza fada tsakanin Hamas da sojojin Isra’ila.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.