Isa ga babban shafi
Isra'ila-Falesdinawa

Isra’ila ta zargi Hamas da sace Yara

Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya zargi Kungiyar Hamas da sace yara kanana guda uku Yahudawa wadanda suka bata a ranar Alhamis a gabar yamma da kogin Jordan. Yanzu haka Jami’an tsaron Isra’ila sun cafke Falesdinawa 80, yawancinsu mambobin Hamas.

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu
Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu REUTERS/Dan Balilty
Talla

“ Hamas ce ta sace yaran” a cewar Netanyahu, yayin da kuma Hamas ta musanta zargin.

Dukkanin yaran ba su wuce 'Yan shekaru 20 ba, kuma ana hasashen an sace su ne a yankin Bathelehem da Hebron.

Sace yaran dai na zuwa ne duka kwanaki goma da aka samu gwamnatin Hadaka tsakanin Hamas da Fatah, matakin da bai yi wa Isra’ila dadi ba.

Kungiyar Hamas da Isra’ila ke gani a matsayin kungiyar ‘Yan ta’adda, tace wannan wani yunkuri ne na kokarin wargaza hadin kan Falesdinawa.

Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya yi Allah waddai da sace yaran tare da kira ga Isra’ila da Hamas su kai zuciya nesa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.