Isa ga babban shafi
Malaysia-China

An tabbatar da cewa jirgin kasar Malaysian nan ya fada teku ne

Hukumomi a kasar Malaysia sun gabatar da bayanan dake hannun su, dake nuna cewa jirgin saman nan mai lamba MH370 daya bace da mutane samada 230, fadawa yayi cikin tekun India.Gabatar da wadannan bayanai yau Talata ya biyo bayan nacewa ne, da dangi da ‘yan uwan fasinjojin suka yi don a nuna bayanan da Gwamnatin ke dogaro dasu, da suka nuna jirgin saman ya fadi amma an kasa gano inda ya fada.A ranar 8 ga wata uku na wannan shekaran ne jirgin saman ya bace da fasinjoji 239 kuma har yanzu ko kusa daya ba a gan shi ba.Akasarin fasinjojin jirgin ‘yan kasar China ne, kuma ya taso ne daga birnin Kaula Lumpur na kasar Malaysiy, zuwa Beijing na kasar China. 

Wasu masu aiki neman jirgin saman kasar Malaysia da ya bace
Wasu masu aiki neman jirgin saman kasar Malaysia da ya bace Reuters/路透社
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.