Isa ga babban shafi
Switzerland

Taron tattalin arzikin duniya a Davos

Yau Laraba ne ake soma yin taron masana tattalin arziki da shugabanin duniya a Davos, da ke kasar Switzerland, inda ake saran shugabanin kasashe 40 da ‘Yan kasuwa sama da 2,000 zasu halarta. Taron na zuwa ne a dai dai lokacin da Hukumar bayar da lamuni ta duniya ke hasashen cewar za’a samu habakar tattalin arzikin duniya sosai a cikin wannan shekara.

Harabar zauren taron tattalin arzikin Duniya a Davos
Harabar zauren taron tattalin arzikin Duniya a Davos REUTERS/Ruben Sprich
Talla

Kafin taron akwai wani rahoto da aka fitar na girman tazara tsakanin attajirai da talakawa a duniya inda aka ce attajiran duniya 85 sun fi rabin mutane duniya arziki.

Wata kungiyar kare hakin talakawa ce ta fitar da rahoton, kuma kungiyar ta yi tsokaci ne akan yadda attajirai ke danne talakawa wajen samar da sauye sauyen da zasu kare muradunsu ba tare da la’akari da talakawan ba.

Kungiyar ta Oxfam tace harajin da attajirai ke dauka be taka kara ya karya ba idan an yi la’akari da kudaden da suke samu.

Babban Ma’audin taron a bana shi ne kokarrin sauya tattalin arzikin duniya ta la’ari da ci gaban kasuwanci da siyasa da kuma zamantakewa.

Akwai kuma shugabannin kasashen duniya sama da 40 da zasu halarci taron da suka hada da shugabannin kasashen da ke takun saka da juna Isra’ila da Iran.

Taron kuma zai tattauna akan makomar ci gaban tattalin arziki a kasashe masu tasowa da kasuwar fasaha da kaulubalen da ake fuskanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.