Isa ga babban shafi
Amurka

Tattalin arzikin kasar Amurka ya girgiza- Masana

Duk da amincewa da Majalisar Dattawan kasar Amurka ta yi da fadada damar karbar bashi, masana tattalin arziki a kasar Amurka sun ce makwanni biyun da aka kwashe ana wannan takaddama tsakanin ‘Yan jam’iyar Democrats da na Republican game da ya shafi tattalin arzikin kasar.

Shugaba Barack Obama na kasar Amurka.
Shugaba Barack Obama na kasar Amurka. REUTERS/Kevin Lamarque
Talla

Hakan kuma a cewar masanan ya kara kaifin tafiyar hawainiyar da tattalin arzikin kasar ke fuskanta tun kamin wannan takadda inda bayanai ke nuni da cewa an yi asarar biliyan 24 na dalar Amurka sakamakon rufe wasu ma'aikatu da aka yi.

Sun kuma kara da cewa akwai alamu karara da suka nuna tabuwar tattalin arzikin kasar suna masu kashedin muddin aka kuma tsunduma cikin irin wannan yanayi a watan Janairun shekara mai zuwa, tattalin arzikin kasar zai kadu sosai.

Wannan bayanan masana tattalin arzikin na zuwa ne jim kadan bayan Shugaba Barack Obama ya saka hanu akan wata yarjejeniya wacce ta kawo karshen takaddamar wacce ta kai ga rufe wasu ma’aikatun kasar saboda babu kudaden tafiyar da su.

A wani sharhi da ya fitar a yau Alhamis, Kamfanin Dillancin labaran kasar China na Xinhua ya zargi kasar Amurka akan kawo tsaiko wajen ci gaban tattalin arzikin duniya.

A yanzu haka Obama ya mika tayi ga daukancin manya ‘yan siyasar kasar da su zo a hada kai domin a farfado da arzikin kasar yana mai cewa ya zama dole a ajiye siyasa a gefe a domin bunkasa harkokin kasar ta Amurka.

A cewar Obama akwai bukatar ‘yan kasar Amurka su sake samun yarda akan shugabannin da suka zaba.

“Ina mai kwadayin na yi aiki da kowa da kowa, ‘yan Democrats ko ‘yan Repiblicans, ‘yan majalisar wakilai ko na dattawa.”

Obama ya kara da cewa a shirye yake ya amince da duk wata shawara da za ta kawo ci gaba ga kasar Amurka.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.