Isa ga babban shafi
Amurka

Har yanzu an kasa samun jituwa akan kasafin kudin Amurka

Rahotanni daga kasar Amurka na nuni da cewa har yanzu ba a samu daidaito tsakanin Shugaba Barack Obama na Amurka da ‘yan majalisun jam’iyyar Repulican ba bayan wani zama na musamman da aka yi a jiya Lahadi domin shawo kan matsalar da ta kunno kai a majalisar game da kasafin kudin kasar. 

Shugaban kasar Amurka Barack Obama
Shugaban kasar Amurka Barack Obama
Talla

Wannan rikici ya doshi mako na uku ken an duk da karatowar wa’adin da aka diba na samar da kudaden gudanar da ma’aikatun tarayyar kasa.

‘Yan majalisun sun gudanar da zaman na musamman ne a kokarin ganin an samu matsaya game da kasafin kudin kasar wanda rashinsa ke kawo barazana ga kasuwannin duniya baya ga ita Amurkan.

Bayanai na nuna cewa idan har wannan takaddama ta kai zuwa 17 ga watan Oktoba hakan zai haifar da rufe baitul malin kasar baki daya yayin da kasuwannin duniya za su girgiza domin a karon farko gwamnatin Obama ba za ta kasa iya gudanar da ayyukanta ga jama'a.

Amurka dai ita ce kasa da tafi kowace kasa karfin tattalin arziki a duniya hakan kuma zai shafi tattalin arzikin duniya baki daya.

Kasar China da Japan wadande ke rike da bashin kasar ta Amurka sama da tiriliyan 2.4 na dalar sun yi kira ga hukumomin Fadar White House da ta yi kokari su kintsa gidansu.

Gwamnan bankin Faransa Christian Noyer ita ma ta yi gargadi akan halin da za a shiga muddin ba a samu matsaya a Amurkan ba.

A yanzu haka dai darajar kudin dalar Amurka ya fadi a nahiyar Asiya.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.