Isa ga babban shafi
Haiti

Mutanen Haiti sun tuna bala’in girgizan kasa

Al’umomin Kasar Haiti sun gudanar da addu’oin cika shekaru hudu da bala’in girgizar kasar da ta hallaka mutane sama da 250,000 a cikin kasar. Shugaban kasa, Michel Martelly, ya jagoranci addu’oin wajen aje firanni a inda aka binne wasu mamatan. Kungiyoyin masu zaman kansu sun ce har ya zuwa yanzu mutane sama da 150,000 na zama a wani waje na wucin gadi, saboda an gaza gyara muhallinsu.

Mutanen Haiti suna bikin juyayin cika shekaru hudu da bala'in girgizan kasa.
Mutanen Haiti suna bikin juyayin cika shekaru hudu da bala'in girgizan kasa. AFP PHOTO/Hector RETAMAL
Talla

A ranar 12 ga watan Janairun 2010 ne girgizan kasa ta shafi kasar Haiti inda Miliyoyan mutane suka rasa gidajensu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.