Isa ga babban shafi
Amurka

Mataimakin shugaban Amurka na ziyarar aiki a kasar Japan

Sabon jakadan Amurka a kasar Japan Caroline Kennedy ce ta karbi Biden a filin jirgin saman birnin Tokyo, kuma a gobe talata ake sa ran zai gana da shugabanin kasar ta Japan.

Mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden
Mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden REUTERS
Talla

Muhimman abubuwan da bangarorin 2 za su tattauna sun hada da takun saka da ake yi kan iyaka tsakanin Japan da China, lamarin da ke ci gaba da zafafa.

Yayin ziyarar yankin, Biden zai kuma gana da shugaban kasar China Xi Jinping a birnin Beijing, kafin ya zarce zuwa birnin Seoul, don ganawa da shugabar koriya ta Kudu Park Geun-Hye.

Ziyarar na zuwa na a makonni 2, bayan China ta takaita shawagin jiragen sama, a yankunan da ke gabashin tetun da ke cikin iyakar kasar ta.

China ta ce duk jirgin saman da zai yi shawagi a yankin da take takaddama da Japan, sai an yi bayani kan dalilan zuwan shi, ya kuma bi dokokin kasar ta.
A ranar laraba, Biden zai nufi birnin Beijing, ranar Alhamis kuma ya isa Seoul.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.