Colombia
Gwamnatin Colombia ta kulla yarjejeniya da 'yan tawayen FARC
Gwamnatin Kasar Colombia ta kulla yarjejeniya da Yan Tawayen FARC wanda zai basu damar shiga harkokin siyasa muddin suka kawo karshen daukar makaman da suka kwashe shekaru 50 suna yi.Wani jami’in diflomasiyar kasar Cuba dake shiga tsakanin tattaunawar da ake a birnin Havana, Rodlfo Benitez, yace sun cimma matsaya kan daya daga cikin manyan batutuwan da bangarorin suke takaddama akai.Yanzu abinda ya rage, shine batun safarar hodar ibilis, biyan diyya da kuma aje makamai.
Wallafawa ranar: