Isa ga babban shafi
Colombia

Colombia zata gabatar da kudurin Dokar samar da zaman lafiya tsakanin gwamnati da ‘yan tawayen FARC.

Shugaban kasar Colombiya Juan Manuel Santos ya bayyana aniyarsa na gabatar da wata ayar doka a gaban majalisar dokokin kasar wace zata samar da dawwamamen zaman lafiya tsakanin gwamnati da tsohuwar kungiyar yan tawayen Farc wace za a mika ga al’ummar kasar domin gudanar da zaben raba gardama.

Mayakan kungiyar 'yantawayen FARC a Colombiya
Mayakan kungiyar 'yantawayen FARC a Colombiya
Talla

A watan Nuwamban shekarar 2012 ne Gwamnatin kasar Colombiya ta cimma wata yarjejeniyar kawo karshen tashin hankalin da yayi sanadiyar mutuwar mutane dubu 200 a cikin shekaru 5.

Idan kuma ya tafi dai dai kamar yadda shugaba Santos ya bukata, al’ummar kasar Colambiya zasu halarci rumfunan zaben raba gardama domin yanke hukumci kan kawo karshen rikicin na kasar Colombiy.

Akan haka shugaba Manuel Santos ya kara da cewa an samu ci gaba a yinkurin da ake yi wajen tabbatar da zaman lafiya a kasar tsakanin gwamnati da 'yan tawayen Farc, kuma nauyi ne da ya rataya a wuyansu wajen ganin sunyi abinda ya dace domin cimma burin da aka sa a gaba, da zai gaggauta kawo saka hannu kan yarjejeniyar zaman lafiyar.

Daga karshe al’ummar kasar colombiya sune keda Wuka da Nama wajen amincewa ko rashin amincewa da yarjejeniyar da aka cimma tsakanin gwamnatin da kuma kungiyar yan Awaren kasar ta Colombiya wato Farc.

Ana sa ran gudanar da zaben raba gardamar ne tare da na 'yan majalisar dokokin kasar a cikin watan Maris din Shekarar 2014 mai shirin kamawa zabubbukan da zasu share fagen shugabancin kasar a cikin watan Mayun wannan Shekara 2014.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.