Brazil ta gudanar aikin leken asirin kasashen Latin a zamanin Soji
Wasu bayanai da aka gano, sun yi nuni da cewa tsohuwar gwamnatin kama karya ta kasar Brazil wadda ta yi mulkin kasar daga 1964-1985, ta gudanar da ayyukan leken asiri akan kasashe makwabtanta da ke yankin Latin Amurka kamar yadda wata jarida da ake bugawa a kasar mai suna Estado de Sao Pauo ta kwarmata.
Wallafawa ranar:
Rahotanni sun ce jaridar ta wallafa wannan labari ne a daidai lokacin da ministan harkokin wajen kasar Antonio Patriota ke shirin yin furuci a game da wannan batu sakamakon yadda tsohon jami’in leken asirin kasar Amurka Edward Snowden ya tsegunta wannan labari ga sauran kasashen duniya.
Jaridar tace wasu takardu a Ofishin babban hafsan Sojin Brazil sun nuna an gudanar da aikin leken asirin dubarun sojin wasu kasashe ne a yankin Latin Amurka.
Kasashen da kuma aka gudanar da binciken dubarun tsarin tafiyar da aikin Sojinsu sun hada da Bolivia da Colombia da Venezuela saboda tunanin za su iya abkawa Brazil.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu