Isa ga babban shafi
Colombia

An kulla yarjejeniyar sulhu tsakanin gwamnati da kungiyar FARC.

Ra’ayoyi sun sha bambam dangane da yarjejeniyar da akala kulla da nufin kawo karshen yakin basasar da ake yi tsakanin ‘yan tawayen kungiyar FARC da kuma gwamnatin kasar Columbia, yakin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla dubu 600 a cikin shekaru 50 da suka gabata.

Zaman sulhu tsakanin gwamnatin Colombia da FARC
Zaman sulhu tsakanin gwamnatin Colombia da FARC Reuters
Talla

Tsohon shugaban kasar ta Columbia Alvaro Uribe wanda a lokacin mulkinsa ya tsananta kai hare-hare a kan wannan kumgiya, ya ce sulhun da aka yi na a matsayin yi wa ‘yan ta’adda afuwa ne.
Kawo yanzu dai ba a bayyana wa duniya abubuwan da ke kunshe a cikin yarjejeniyar sulhun da bangarorin biyu suka cimma ba, to sai dai rahotannin na cewa gwamnati ta amince da bai wa yankunan da ‘yan tawayen ke fafatawa da gwamnati a cikinsu karfin ikon mallakar filaye da kuma kaddamar da wasu ayyuka da suka shafi yaki da talauci a yankunan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.