Isa ga babban shafi
Palasdinu

Faransa ta nuna goyon bayanta ga Palasdinawa

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius wanda ke gudanar da ziyara a yankin Gabas ta Tsakiya, ya tattauna da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas a garin Ramallah, a wani mataki da Faransa ta bayyana shi da cewa na nuna goyon baya ne ga tattaunawar zaman lafiyar da ake yi tsakanin Palasdinawa da kuma Yahudawan Isra’ila.Fabius ya ce al’ummar Palasdinu na da hakkin mallakar kasa ta kansu, wadda za ta za su rayu kafada da kafada da Isra’ila a cikin tsaro da kuma zaman lafiya.Ministan na harkokin wajen na Faransa ya ce ci gaba da gina gidajen da Isra’ila ke yi, a gabar yammacin Kogin Jordan abu ne da ya sabawa ka’ida. 

Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius tare da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas
Ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius tare da shugaban Palasdinawa Mahmoud Abbas REUTERS/Mohamad Torokman
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.