Palasdinawa sun yi bukin cika shekaru 46 da yaki da Isra'ila
Hukumomin Palasdinu sun yi bukin cika shekaru 46, da fara yaki da kasar Isra’ila, inda suka nemi a dora duk wata tattaunawa da hukumomin birnin Tel Abiv, kan amincewa da iyakokin kasar ta Palasdinu, kafin mamayar da Yahudawan suka yi a shekarar 1967. Babban mai shiga tsakani na bangeren Palasdinawan Saeb Erakat ya ziyarci kauyuka 3, da mazauna suka tsere, yayin da kasar ta Isra’ila ta mamaye su a yakin da ta shafe kwanaki 6, ana gwabzawa da sojojinn kasashen Misrah Jordan da Siriya.Kasar ta Isra’ila ta mamaye da yammacin kogin Jordan, da kuma gabashin birnin Jerusalem a zamanin yakin, da Palasdinawa suka bayyana a matsayin koma baya garesu.Mr Erakat yace halin da Palasdinawa dubu 5 suka fada a yakin na shekarar 1967, sakamakon fidda su daga kauyukan nasu ne, ke ci gaba da fada musu a yankin yammacin lgin Jordan a wannan zamanin.Ya jaddada bukatar dakatar da gine ginen da Yahudawa ke yi a yankunan Palasdinawa, tare da mika dukka iyakokin da ake da su kafin yakin, a matsayin matakin farko na tattaunawa da Isra’ila.sai dai a nata bangaren, kasar ta Isra’ila ta nemi a ci gaba da tattaunawa ba tare da gindaya wani shardi daga bangaren Palasdinawan ba.A watan Satumban shekarar 2010 wattaunawa tsakanin bangarorin 2 ta ruguje, sakamakon rashin fahimtar juna kan batun na kan iyakoki.
Wallafawa ranar: