Isa ga babban shafi
Venezuela

Kotu ta umurci a sake duba na'urorin da aka yi zabe da su a Venezuela

A kasar Venezuela kurar siyasa ta dan lafa bayan da hukumar zaben kasar ta amince da sake binciken na’urorin da aka gudanar da zabe da su a kasar, amma ba za a sake kidaya kuri’un zaben shugabancin kasar da aka gudanar a kasar ba.

Nicolas Maduro, na gaisawa da wasu shugaban Latin Amurka bayan rantsar da shi.
Nicolas Maduro, na gaisawa da wasu shugaban Latin Amurka bayan rantsar da shi. REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

A jiya juma’a 19 ga wannan wata ne shugaban kasar Nicolas Maduro ya yi rantsuwar soma aiki, bikin da ke da matukar muhimmanci a gare shi, inda yake sa ran ganin an samu raguwar yawan kasashen duniya da ke da shakku a kan zabensa a matsayin shugaban kasar ta Venezuela.

Shi dai Maduro, ya gaji marigayi Hugo Chavez ne mai ra’ayin gurguzu, to sai dai ‘yan adawa sun yi watsi da nasarar da aka ce ya samu a zaben, suna zargin cewa an tafka magudi ne kawai.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.