Isa ga babban shafi
Venezuela

Rikici ya barke a Venezuela bayan tabbatar da Maduro a matsayin wanda zai gaji Chavez

‘Yan sanda sun yi arangama da masu zanga-zangar adawa da sakamakon zaben shugaban kasar Venezuela da aka bayyana sunan Nicolas Maduro a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasa bayan mutuwar Hugo Chavez.

Dalibai a Birnin Caracas, magoya bayan Henrique Capriles da ke bangaren adawa
Dalibai a Birnin Caracas, magoya bayan Henrique Capriles da ke bangaren adawa REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

Bayan bayyana sakamakon zaben aka samu barkewar rikici tsakanin ‘Yan sanda da masu zanga-zanga a Caracas babban birnin kasar.

Dan Takaran adawa da ya sha kaye a zaben, Henrique Capriles, ya bukaci sake kidayar kuri’un da yace an tafka magudi, inda kuma ya ke barazanar sanya magoya bayansa su gudanar da zanga zanga.

Capriles yace akwai zarge zarge sama da 300,000 da ya dace a sake duba su, amma hukumar zaben kasar tace alkalami ya bushe, inda ta bukaci amincewa da sakamakon zaben.

Zaben dai ya biyo bayan mutuwar Hugo Chavez wanda ya mutu a ranar 5 ga watan Maris.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.