Isa ga babban shafi
Venezuela

Ana gudanar da zaben shugaban kasa a Venezuela

A yau lahadi, al’ummar kasar Venezuela na gudanar da zaben shugaban kasa domin maye gurbin tsohon shugaban kasar Hugo Chavez wanda ya rasu a cikin kwanakin da suka gabata.

Mataimakin shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro da Capriles.
Mataimakin shugaban kasar Venezuela, Nicolas Maduro da Capriles. REUTERS/Carlos Garcia Rawlins
Talla

Zaben na yau wanda shi ne zai fayyace makomar salon mulkin irin na masu ra’ayin Bolivar wanda Chavez ya asassa, akwai ‘yan takara da dama da suka hada da shugaban kasar na riko wanda kuma ke ikirarin kare manufofin tsohon shugaban marigayi Chavez wato Nicolas Madura da kuma babban abokin hamayyarsa kuma gwamnan jihar Miranda Henrique Capriles.
Maduro, dan kimanin shekaru 50 a duniya tsohon direban motar bas ne, kuma ya gudanar da yakin neman zabensa ne ta hanyar jaddada cewa zai ci gaba da kare manufofin tsohon shugaban kasar Hugo Chavez matukar dai ya yi nasara. A halin yanzu ai Maduro ne ake kallon a matsayin wanda zai yi nasara a zaben duk da cewa wasu manazarta na hasashen cewa komai na iya faruwa a lokacin wannan zabe na yau.
Venezuela dai na a matsayin muhimmiyar kasa musamman ma a fagen tattalin arziki sakamakon dimbin arzikin mai da Allah ya ba ta, yayin da tsohon shugaban Hugo Chavez ya yi amfani da matsayina da kuma wannan arziki domin yada manufofinsa a cikin sauran kasashen da ke yankin na Latin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.