Isa ga babban shafi
MDD

Bukin Ranar Ruwa a Duniya

A ranar 22 ga watan Maris ne ake bukin ranar ruwa a Duniya, amma Miliyoyan mutane ne ake gudanar da bukin ba tare da su ba saboda katsewar ruwan sha a yankunansu. Wata cibiyar bincike a Amurka tace sama da mutane Biliyan ne ke fama da matsalar ruwa a Duniya.

Tutar  Majalisar Dinkin Duniya game da bukin samar da ruwa a Duniya
Tutar Majalisar Dinkin Duniya game da bukin samar da ruwa a Duniya DR World Water Week
Talla

Wani hasashen masana ya ce nan da shekarar 2015 ,mutane sama da Biliyan daya da Miliyan 8 ne zasu ci gaba da rayuwa a yankunan da matsalar ruwa za ta shafa.

03:48

Matsalar Ruwa a Najeriya

Shehu Saulawa

A bana an bayyana cewa sama da mutane Biliyan ne ke rayuwa a yankunan da ke fama da matsalar ruwa.

Kuma masana sun ce lamarin zai yi kamari anan gaba saboda ci gaba da samun yawaitar mutane a duniya

Masanan sun kalli matsalar ne ta fuska biyu, inda suka ce ana samun matsalar ne ta yanayin kasa da muhalli. A daya bangaren kuma suka ce ana samun matsalar ne saboda sakacin gwamnatoci musamman kasashen Afrika da matsalar ta fi kamari.

Majalisar Dinkin Duniya tace nan da shekarar 2050 yawan mutane zai karu daga Biliyan Bakwai zuwa sama da Biliyan Tara. Lamarin da ake ganin barazana ce ga kashi biyar na al’ummar duniya da ke fama da matsalar ruwa.

03:57

Matsalar Ruwa a Nijar

Salisu Isah

Akan haka ne aka yi kira ga hukumonin kasashe da matsalar ta shafa su dauki mataki, domin matsalar ruwa zai shafi manoma wajen samar da abinci da makamashi da kuma masana’antu da ke amfani da ruwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.