Isa ga babban shafi
Philippine-Syria

Philippines ta nemi sakin ‘Yan kasarta da aka yi garkuwa da su a Syria

Gwamnatin kasar Philippines ta yi kira ga ‘Yan tawayen Syria su gaggauta sakin ‘Yan kasarta 21 da suka yi garkuwa da su wadanda ke aikin sa ido a rikicin kasar. Jami’an na Majalisar Dinkin Duniya, an yi garkuwa da su ne a wani tsauni da ke kan iyaka tsakanin Syria da Isra’ila inda suke sa ido wajen ganin an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta.

Jamian Majalisar Dinkin Duniya akan iyakar Isra'ila da Syria a Golan
Jamian Majalisar Dinkin Duniya akan iyakar Isra'ila da Syria a Golan REUTERS/Baz Ratner
Talla

Ministan harakokin wajen Philippines yace ma’aikatan suna cikin koshin lafiya kuma gwamnatin kasar na kan tattaunawa da ‘Yan tawayen domin ganin an sake su.

Wani hoton Bidiyo da aka yada a Intanet ya nuna wani mutum kusa da mota yana ikirarin shi Dan tawayen Syria ne.

A wata wasika, ‘Yan tawayen sun ce sai dakarun Bashar al Assad sun fice daga kauyen Jamla kafin su saki ma’aikatan da ke hannunsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.